Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari a yankunan kudancin birnin Gaza da kuma tsakiyar Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza. A sa'i daya kuma, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a arewacin sansanin Al-Shati da ke yammacin birnin Gaza da yankunan gabashin birnin ciki har da kewayen mahadar Shuja'iyah.
A arewa maso yammacin Gaza sojojin mamaya sun tayar da wasu motoci masu sulke tare da tayar da bama-bamai a unguwar Sheikh Radwan tare da gudanar da ayyukan lalata da dama a wannan yanki da kuma kan titin Al-Jala. Akwai kuma rahotannin fashewar wasu bamabamai da aka jefa a unguwar Tel Al-Hawwi da ke kudu maso yammacin birnin Gaza.
Your Comment